6 Satumba 2024 - 18:24
Jordan: Ta Yi Kira Da A Haramta Sayar Da Makamai Ga Isra'ila

Ministan harkokin wajen kasar Jordan yayin da yake goyon bayan matakin da Birtaniyya ta dauka na dakatar da lasisin aika nau'ikan makamai iri 30 ga gwamnatin sahyoniyawa, ya bukaci dukkanin kasashen duniya da su hana sayar da makaman soji zuwa wannan gwamnatin.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na IRNA bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazeera cewa, Ayman al-Safadi ya ce: Birtaniyya ta yi abin da ya dace ta hanyar dakatar da wasu lasisin fitar da makamai zuwa Isra'ila.

Ya jaddada cewa: Muna rokon dukkan kasashe da su sanya dokar hana sayar da makamai zuwa Isra'ila.

Al-Safadi ya kara da cewa: Idan ba’a aiwatar da dakatar da lasisin fitar da makamai zuwa Isra'ila ba, Benjamin Netanyahu ba zai dakatar da kai farmakin da yake kai wa Gaza da yammacin kogin Jordan ba.

A cewar IRNA, a kwanan baya ma'aikatar tsaron Burtaniya ta sanar da cewa: A cikin lasisi 350, mun dakatar da lasisin kusan nau'ikan makamai 30 da sojojin Isra'ila ke amfani da su a yakin da ake yi a Gaza.

Ma'aikatar ta kara da cewa: "Akwai bayyanannun hatsarin cewa ana iya amfani da kayayyakin da sojoji ke fitarwa zuwa Isra'ila ta hanyar da ta ci karo da dokar jin kai ta kasa da kasa."

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanar da mayar da martani ga wannan mataki na Birtaniya: Matakin da Birtaniyya ta dauka na dakatar da ba da izinin mallakar makamai iri 30 ga Isra'ila kuskure ne kuma ba zai canza matakin da Isra'ila ta dauka na fatattakar Hamas ba.

A cikin wannan bayani an bayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan za ta yi nasara a yakin da ta ke yi da Gaza da makaman Birtaniya ko ba tare da su  ba.

A cikin wannan bayani, an kuma jaddada cewa: Matakin na Biritaniya zai kara karfafawa kungiyar Hamas ne kawai, wadda ta kama sama da mutane 100, wadanda 5 daga cikinsu 'yan Birtaniya ne.

Biritaniya dai na cikin jerin kasashen da suka dade suna kawance da gwamnatin sahyoniyawan, wadanda gwamnatinsu ke fuskantar matsin lamba na cikin gida na ta daina fitar da makamai zuwa yankunan da Isra’ila ta mamaye.

Bayan binciken da gwamnatin Birtaniya ta gudanar nan take bayan gagarumin nasarar da jam'iyyar Labour ta samu a zabukan kasar da aka gudanar a baya-bayan nan, gwamnatin kasar ta cimma matsaya kan cewa akwai yiwuwar gwamnatin sahyoniyawan tana kan keta dokokin kasa da kasa.

Tun a watan Oktoban shekarar 2023 ne gwamnatin sahyoniyawan tare da goyon bayan Amurka da Birtaniya da sauran kawayenta na yammacin duniya suke ta kaddamar da mummunan yaki kan al'ummar Zirin Gaza, kuma sama da Palasdinawa 40,000 ne suka yi shahada a wannan yakin.

A cikin wannan yakin, baya ga rushe-rushe da yunwa da ta yi sanadiyar mutuwar daruruwan yaran Palasdinawa da ake yi wa kallon daya daga cikin mafi muni a duniya, fiye da Palasdinawa 10,000 kuma sun bace.